Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Katin Zama Cikin Amurka Na Iya Dawowa Kasar - John Kelly


 John Kelly sakataren tsaron cikin gida
John Kelly sakataren tsaron cikin gida

Ministan tsaron cikin gida na Amurka John Kelly, yace ya hakikance barin wadanda suke da katin zama a Amurka su dawo cikin kasar yana daga cikin muradun kasa, kuma yin hakan bai sabawa umarnin da shugaba Trump ya bayar kan 'yan gudun hijira da bakin haure ba.

Bayanin da ministan ya bayar dazu cikin dare, ya bada haske kan rudani dangane da umarnin na shugaban Amurka wanda ya kayyade batun shige da fice. Matakin na shugaban kasa ya tsaida shiga da fita na tsawon kwanaki 90 daga wasu kasashen musulmi bakwai da suke samarda 'yan ta'adda.

Shugaba Trump ya kare umarnin nasa a dai dai lokacinda duniya baki daya take kuruwa kan dokar da bayar, yace matakin ba kan addini bane, amma batu ne na "ta'addanci da zummar kare kasarmu".

Shugaban na Amurka ya lura cewa tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya ambaci wadannan kasashe bakwai Iran da Iraqi, da Libya, da Somalia, da Sudan, da Syria da kuma Yemen a zaman sarsalar ta'addanci.

Ya kara da cewa fiye da kasashen musulmi 40 dokar bata shafe su ba, daga nan sai ya caccaki kafafen yada labarai saboda kiran umarnin nasa a zaman hana musulmi shigowa Amurka.

Ahalinda ake ciki kuma, Fadar White House tace, shugaba Trump da sarki Salman bin Abdel Aziz sun yarda kan bukatar goyon bayan kirkiro da tudun mun tsira a Syria da Yemen.

Shugabannin biyu sun tattauna da ta wayar tarho jiya Lahadi, abund a ya kara tabbatarda dadaddiyar dangantaka tsakanin Amurka da Saudiyya.

Haka nan ana sa ran shugaba Trump yayi magana da wasu shugabanni a yankin Gabas ta Tsakiya da ma wasu sassan duniya.

XS
SM
MD
LG