Ayarin farko na tallafin kayan abinci,magunguna, barguna,kayan masarufi na agajin gaggawa na gwamnatin tarayya sun isa tsaunin Mamblia na karamar hukumar Sardauna dake jihar Taraba da tashe-tashen hankula ya shafa.
Jagoran tawagar da ta hada da hukumar kai daokin gaggawa ta kasa NEMA Birgedya Janar S.P Ohemu ya fadawa ‘yan gudun hijiran gwamnati tarayya na sane da matsalolin da rikicin yankin ya jefa su ciki kuma tana daukan matakai na maido da zaman lafiya domin basu sukunin komawa muhallansu.
Hafsan sojan wanda ya yaba da matakin da sarkin Mambila ya dauka na tausayawa ta hanyar baiwa ‘yan gudun hijira sama da dari biyu mafaka a fadarsa, ya ce wannan yana cikin dalilin da tawagar ta yanke shawarar ya zama na farko da zai amshi tallafin.
Daga cikin ‘yan gudun hijira da suka anfana da tallafin Malama Maryam da Shua’ibu Alhaji Hamza farin cki suka nuna da tallafin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar wanda suka bayyana cewa sun wadatar.
Mai martaba sarkin Mambila Dokta Shehu Audu Baju da yake amsar kayan tallafin a fadarsa ya ba da tabbacin kamanta adalci wajen rabon kayan wanda inji shi zai taimaka da agajin da gwamnatin jihar Taraba ke baiwa ‘yan gudun hijiran tun daga lokacin da rikicin ya barke.
Yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira saman da dubu hudu dake warwatse a tsaunin Mambilan har da makwabciyar Najeriya a Jamhuriyar Kamaru da bayanai ke nua na cikin hali na tagayyara.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5