ABUJA, NIGERIA - Kayayyakin da farashin su suka tashi a watan Afrilun bana, sun hada da Shinkafa, Garri, Wake, Tumatur, Albasa, Burodi, Nama da dai sauransu, wanda jimillar su ya kai hauhawar farashin kayayyaki da kaso 40.5
Rahoton na NBS, ya kara da cewa, farashin Shinkafa ya tashi da kaso 156 idan aka kwatanta shi da farashinsa a shekarar 2023, inda ake sayar da kilo daya akan Naira 547, yanzu kuma ake sayar da kilon akan Naira 1,399.
Sai kuma farashin Garrin kwaki da ake masa lakabin “sai ta baci ake nemansa” wanda shima farashinsa ya tashi da kaso 135 idan aka kwatanta da shekarar 2023, wato daga Naira 363 zuwa Naira 1,554.
Sai kuma farashin Tumatur da ya tashi da kaso 132 idan aka kwatanta shi da farashinsa a shekarar 2023, daga Naira 485 zuwa Naira 1,123.
Shima farashin wake yayi tashin da bai taba yi ba, inda ya karu da kaso 125, a shekarar da ta gabata farashin waken an sayar dashi akan Naira 616, yanzu kuma farashinsa ya kai 1,388 akan kowanne kilo.
‘Ƴan Najeriya dai na bayyana takaicinsu game yadda farashin kayayyakin ke ci gaba da tashi a kasar.
A hirarsa da Muryar Amurka, Dr. Isa Abdullahi Kashere, malami kuma masanin tattalin arziki dake Jami’ar Tarayya ta Kashere a Jihar Gombe, ya dora alhakin hauhawar farashin kaya a kasar ga ‘ƴan kasuwa ne.
Kashere, ya ce “wasu 'yan kasuwa na amfani da wannan dama wajen sayen kayayyakin masarufi dake kasuwa, kuma su boye shi domin cin kazaman riba nan gaba.
Yanzu dai hankulan ‘ƴan kasar na ci gaba da hankoron ganin irin matakan da gwamnatin tarayya za ta dauka domin kawo karshen wannan matsala ta hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Saurari cikakken rahoton Rukaiya Basha:
Your browser doesn’t support HTML5