Al’ummar yankin sun bayyana irin hadarin dake tattare da bin hanyoyin yankunan, lamarin da ke kawo koma baya ga harkokin jama’a. Sun kuma yi kira ga hukumomi su kawo musu dauki kana a basu kariya daga ayyukkan ‘yan bata garin.
Gwamnatin jahar Kaduna dai ta sha alwashin daukar matakan shawo kan wadannan matsaloli. A cikin hirarshi da Muryar Amurka, Malam Samuel Aruwan kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jahar Kaduna ya bayyana cewa gwamnati na kokari.
“Ya ce akwai matakai daban daban da gwamnati da jami’an tsaro ke dauka, ana kuma sa ran kwalliya zata biya kudin sabula. Ya kara da cewa gwamnati na sane da kwararowar ‘yan bindiga daga yankunan Zamfara kuma akwai dabaru da ake dauka da za a bayyan nan gaba”.
Tun bayan kaddamar da hare-haren aka tura rundunar sojan Najeriya a yankunan jahohin Katsina da Zamfara sai wasu al'umar yankunan kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa suna ta kokawa game da hauhawar hare haren'yan bindigan da su ke ganin daga yankunan da sojoji ke kai hare haren su ke gudowa.
Ga rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:
Your browser doesn’t support HTML5