Kakakin Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta jihar Katsina (KSIRS) Sada Shu’aibu ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi ranar Alhamis a Katsina.
Ya ce matakin yana da matukar muhimmanci wajen karkata tsarin biyan haraji da gudanar da ayyuka domin bunkasa samar da kudaden shiga ba tare da an salwantar da su ba.
Shugaban hukumar ya kara da cewa gwamnatin jiha ta samar da manhajar ne domin inganta tattara kudaden shiga da jihar ke samu.
A cewarsa tsarin manhajar zai baiwa masu biyan haraji damar yin rijista da ma’aikatar, wanda hakan kuma zai kauda zargi a tsakanin ma'aikatan domin kudaden za su rinka shiga asusun gwamnatin jihar kai tsaye.
“Tare da sabon tsarin, masu biyan haraji za su iya yin rajista, yin lissafi, da kuma biyan harajinsu ta hanyar wayar hannu ko kwamfutar tafi-da-gidanka,” inji shi.