Kasuwar Bajakoli A Birnin Jos Ta Hada Kan ‘Yan Najeriya Da Sauran Kasashe

Bajakoli

Kasuwar bajakoli da aka gudanar da garin Jos ta habaka zamantakewar al’ummar jihar da wasu jihohin Najeriya da kuma kasashen duniya.

Kimanin ‘yan kasashen waje fiye da 10 ne suka halarci kasuwar bajakolin, yayin da ‘yan kasuwar sauran jihohin Najeriya suka halarci bajakolin don gudanar da kasuwancin su.

Wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji, ta zanta da ‘yan kasuwa daban daban da suka halarci bajakolin, Abdullahi Ibrahim wanda ya zo daga jamhuriyar Nijar, yace wasunsu dayawa sunki zuwa domin suna tunanin har yanzu akwai tashin hankali, wanda yanzu ya ga sabanin hakan zaman lafiya.

Shima Yarima Dan Dauda, ‘dan asalin jihar Kaduna yace an samu zaman lafiya sosai idan aka kwatanta da bajakolin da suka ziyarta a shekara ta 2010, inda suka rika jin fashewar boma bomai.

Kawuwar bajakolin dai ta hada mabiya addinai daban daban da kabilu daban daban ba tare da samun wani tashin hankali ba

Kwamishinan ma’aikatar kasuwanci da ma’aikatu a jihar Plateau Mr. Ezekiel Daju, yace sun shirya bukin bajakolin ne domin nunawa duniya an samu dawwamamman zaman lafiya a jihar Plateau.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasuwar Bajakoli A Birnin Jos Ta Hada Kan ‘Yan Najeriya Da Sauran Kasashe - 3'40"