Daliban maza da mata da suka nufi babbar sakatariyar gwamnatin tarayya suna kira da babbar murya a sako masu shugabansu da uwargidansa.
Daliban sun rike manyan hotunan Shaikh Ibrahim El-Zakzaky da rubutun a sakoshi a turance.
Abdullahi Muhammad Musa sakataren daliban ya zanta da Muryar Amurka bayan da 'yansanda suka tarwatsa taron saboda wai suna zanga zangar ce ba tare da izinin ba.
Abdullahi Musa yace dole ne su fito suyi zanga zanga saboda inji jami'an tsaro ko 'yansanda wai sun ajiye shishugaban nasu ne domin kare lafiyarsa. Yace ta yaya zasu kare mutumin da suka harba. Yace jami'an tsaro sun fada da bakinsu cewa shugaban nasu bashi da lafiya suna yi masa magani.
Acewar Abdullahi masu zuwa ganin shugaban nasu da suka hada da dansa sun ce idonsa guda ma baya gani dashi kana likitan dake kula dashi yace shi ya gama aikinsa.
Kungiyoyin ahalusunna irin su IZALA sun kara fayyace sukar da suke yiwa 'yan shiya ta shafi zagin sahabai ne kan Manzon Allah. Amma bisa tsarin mulkin Najeriya babu wanda aka hana gudanar da addininsa matukar ba zai tada fitina ba.
Shaikh Muhammad Haruna Gombe yace kowane irin addini ne gwamnati tana da daman ta sa ido ta tabbatar wajen gudanar da addinin ba'a ci zarafin al'umma ba, ba'a hana al'umma zaman lafiya ba, ba'a kuma jawo tabarbarewar doka da oda ba.
Acewar Shaikh Haruna Gombe yayinda su suke goyon bayan bin doka ita kungiyar Shiya tana goyon bayan tabarbarewar doka ne tare da harzuka tashin hankali.
Batun cewa gwamnatin Kaduna ta soke addini yace wannan ba gaskiya ba ne. Gwamnatin Kaduna bata soke addinin musulunci ba amma ta soke duk wata kungiyar da zata tada hankalin jama'a. Matakin gwamnatin Kaduna bai hana kungiyar Shiya yin wa'azi ba kan abun da ta gani ba gaskiya ba ne bisa ga addinin musulunci.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.