Lamari na baya-bayan nan shine wanda ya faru ranar Juma’a a garin Mutunji dake jihar Zamfara, lokacin da yan bindiga suka afkawa garin tare da yin awon gaba da mutane sama da 100.
Tun farko dai an sami wata hatsaniya tsakanin mutanen yankin da yaran wani gagarumin dan bindiga da ake yiwa lakabi da Damina, daga nan ne Damina ya nemi al’umomin Mutunji da su hada masa harajin Naira Miliyan 50, al’umomin Kwana su biya miliyan 30, su kuma na sabon garin Mahuta su hada miliyan 20, sai kuma unguwar Kawo miliyan 10.
Damina ya baiwa al’umomin yankunan wa’adin mako biyu da su hada kudaden da jimillarsu ta kai Naira miliyan 110. Ranar Juma’a wa’adin ya cika ba tare da an hada kudaden ba, wanda hakan ya sa ya tara mutane sama da 100 a garin Mutunji ya korasu cikin daji.
Wani jami’in gwamnatin jihar Zamfara da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatarwa da Sashen Hausa faruwar lamarin, inda ya ce yanzu haka gwamnati na ci gaba da kokarin ganin ta kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.
A cewar shaidun gani da ido, dan bindaga Damina ya sanar da al’ummar Mutunji zai koma domin ya yi abin da ya kira “Askin Kwalba” amma kafin lokacin jami’an soji sun kai dauki garin.
Domin Karin bayani saurari rahotan Sani Shu’aibu Malumfashi.
Your browser doesn’t support HTML5