Kasashen Yammacin Afirka Na Kokarin Shawo Kan Cutar Mashako

Ana yi wa wani jariri rigakin cutar mashako

Akalla mutum 573 cikin 11,640 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya sun mutu tun bayan barkewarta a watan Disambar 2022.

Hukumomi a kasashen Yammacin Afirka da dama na kokarin shawo kan cutar mashako da ta barke a yankin, ciki har da Najeriya, inda wani babban jami’in lafiya ya fada a ranar Alhamis cewa an yi wa miliyoyin mutane rigakafi, domin cike gibin rigakafin cutar.

Akalla mutum 573 daga cikin 11,640 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya sun mutu tun bayan barkewarta a watan Disambar 2022.

Ko da yake, jami’ai sun kiyasin cewa adadin a yanzu ya ragu saboda samar da ingantattun matakan jinya.

A Jamhuriyar Nijar kuma da ke makwabtaka da Najeriya, mutum 37 ne suka mutu cikin mutum 865 da suka kamu da cutar ya zuwa watan Oktoban da ya wuce, yayin da a kasar Guinea aka ba da rahoton mutuwar mutum 58 daga cikin 497 da suka kamu tun bayan barkewar cutar a watan Yuni.

Ya zuwa yanzu dai an samu rahoton kamuwa da cutar mai saurin yaduwa a jihohi 20 cikin 36 na Najeriya.

A Najeriya, kashi 42 cikin 100 na yara ‘yan kasa da shekaru 15 ne kawai ke samun cikakkiyar kariya daga kamuwa da cutar ta mashako, a cewar wani bincike na gwamnati.