Kwamitin kasashen yankin Sahel ya yanke shawarar hanzarta ayyukan ceto Tafkin Chadi da Kogin Niger daga mawuyacin halin da suke ciki.
A dauki wannan matsaya ce domin al'ummar yankin zsu amfana da albarkatun da Allah ya yankin.
Ministan bunkasa ayyukan noma da kiwo a Niger, Alhaji Albade Abuba, ya ce kogin tafkin Chadi kasa ta fara cika shi dalili ke nan da shugabannin suka ba da umurnin a nemi hanyar da za'a ceto kogin tun yanzu.
A cewarsa, haka ma kasa ke yi wa Kogin Niger barazana yana mai cewa asarar wadannan kogunan zai sa rayuwa a yankin ta yi wuya.
Shugaban kasar Burkina Faso Kabore da ke karban shugabancin kwamitin kasashen daga shugaban kasar Mali Bubakar Keita ya gargadi kasashen su gaggauta biyan kudaden karo-karon da ya wajaba a kansu domin a samu a gudanar da ayyukan kungiyar kamar yadda ya kamata.
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5