NIAMEY, NIGER - Amma akwai ayar tambaya dangane da hanyoyin samun kudaden gudanar da sabuwar rundunar a bisa la’akari da aka raba gari tsakanin sojojin da ke mulki a kasashen uku da wadanda suka saba basu tallafi a wannan fanni.
A karshen taron kwamandojin rundunonin mayakan Nijar, Mali da Burkina Faso da ya gudana a birnin Yamai ne kasashen uku suka sanar cewa sun kafa rundunar hadin guiwar kasashen kawancen AES da nufin kara jan damarar yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Janar Moussa Salao Barmou babban kwamandan rundunar mayakan Nijar, ya ce mun kai ga kafa rundunar hadin guiwar kasashen AES ne wace za ta fara aiki nan ba da jimawa ba domin tunkarar kalubalen tsaro a yankinmu.
Mai sharhi akan sha’anin tsaro Moustapha Abdoulaye na kallon matakin kasashen na AES da mahimmanci.
Hada karfin soja dabara ce da ka iya bai wa kasashen uku damar tunkarar barazanar da suke fuskanta daga ciki da wajen yankin inji kwararren kan sha’anin tsaro Abass Moumouni, abinda ke da kwarin guiwa a game da tasirin da rundunar ka iya yi a fagen daga.
Juye-juyen mulkin da aka fuskanta a kasashen na Nijar, Mali da Burkina Faso a shekaru uku na baya-bayan nan sun yi sanadin mayar da su saniyar ware, lamarin da hasashen zai iya haddasa cikas wajen samun kudaden gudanar da sabuwar rundunar ta AES kwatankwacin matsalolin da aka yi fama da su a zamanin G5 Sahel.
Sababbin salon yakin da kungiyoyin ta’addancin Sahel ke bijiro da su abu ne da aka yi amannar cewa karfafa matakan soja na iya tasiri kansu, to amma masana na shawartar masu ruwa da tsaki akan bukatar maida hankali kan ayyukan kyautata rayuwar talakkawa.
A watan Satumban 2023 ne kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso suka bada sanarwar kafa kungiyar kawance ta AES wacce a karkashinta suka ayyana cewa zasu gudanar da ayyukan hadin guiwa a fannoni da dama, farawa da matsalolin ta’addancin da suka addabi baki dayan yankin na Sahel yau shekaru sama da 10.
Saurari cikakken. Rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5