Shugaba Donald Trump na bugawa shuwagabannin gabas ta tsakiya da dama waya kafin a fitar da wata sanarwa , watakila zuwa gobe laraba, kan cewa Amurka zata amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.
Sanarwa daga fadar white House ta bayyana cewa shugaba Trump na tattaunawa da Fiyani Ministan Isra’ila Benjamin Natanyahu, da shugaban palasdinawa Mahmoud Abbas da kuma sarkin Jordan Abdallah, da safiyar yau, zai kuma kira sauran shuwagabannin yankin daga baya.
Babu wata takamaimiyar Magana data fito daga white house akan tattaunawar amma kafar yada labaran Palasdinu, ta bada rahoton cewa shugaba Trump, ya ba Abbas tabbacin fitar da sanarwa akan birnin kudus na tafe.
Kasashen larabawa da na Musulmi sun yi gargadin fitar da sanarwar na iya bata kokarin da Amurka ke yi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Larabawa da kasar Isra’ila. Babban shugaban Paladinawa, Nabil Shaath, y ace baza a sake daukar shugaba Trump, a zaman mai shiga tsakani na gaskiya ba.
Shugaban Turkiyya, Rajab Tayyib Erdowan, yayi barazanar cewa zai tsinke hulda da kasar Isra'ila, muddin Trump ya amince da Qudus a zaman babban birnin Isra'ila.