Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci Gaba Da Rike Mataimakin Shugaban Yankin Catalonia Na Spain A Gidan Kaso


Masu zanga zanga don a saki 'yan fafutukar da aka rike
Masu zanga zanga don a saki 'yan fafutukar da aka rike

Wadansu yan siyasar Catalonia sun samu fitowa daga gidan kaso inda wau yan fafutuka da mataimakin shugan yankin suka kasa fitowa a hukuncin da mai shari'a ya yanke.

Wani alkalin kotun kolin Spain mai shari'ar wata kotun ya bada umarni a saki wasu 'yan siyasar Catalonia su shida da ake tsare da su a gidan yari a yau litinin, amman yaki amincewa a saki wasu masu fafutuka biyu da wadansu membobin gwamnatin shiyyar biyu wadanda suka hada da mataimakin shugaban kasar.

Mai shari'a Pablo Llarena ya bada umarnin a cigaba da rike mataimakin shugaban Catalonia da aka tsige, wato Oriol Junqueras, da tsohon ministan harkokin cikin gida Joaquim Forn da shuwagabannin kungiyoyin wariya biyu na Catalonia da su ci gaba da zama a gidan kaso ba tare da anyi belin su ba.

A bayanin da kotun kolin ta bayar, mai shari'ar yace duk da cewar babu hadarin wadanda ake karar zasu bar kasar, amman dole a gani ko alkawarin da sukayi na cewar zasu bi dokokin kasar Spain kuma su daina neman ballewa daga ita gaskiya ne. Alkalin ya bada belin 'yan siyasa shida kowanne akan dalar Amurka 118,000. wannan hukuncin ya basu damar shiga yakin neman zabe a zaben da za'ayi a ranar 21 ga watan Disamba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG