Yau Littini Kasashen Rasha da China sun nuna sha'awarsu ta ganin an sasanta game da halin dar-dar dake tattare da batun makami mai linzami na kasar Korea ta Arewa.
Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergei Lavrov ya fada wa kafar sadarwa ta gwamnati cewa ba wanda zaiso yaga cewa an kai ga gwabza yaki zirin na Korea,Kana yayi fatar cewa Amurka ba tana shirin ganin tayi anfani da karfin soja bane wajen warware wannan matsalar.
Haka ita ma mai maganba da yawun ministan harkokin wajen kasar China Hua Chunying ta fada yau littinin cewa tana fata duka kasashen dake da ruwa da tsaki zasu kokarta suga cewa sun samar da hanya ta sadidan ta zai rage wannan halin zaman kila wakala da ake yi game da wannan lamari domin samun maslaha.
China tace sabon takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya tasa bai kamata ace ya zama mai tasiri ba ga farar hular kasar ta Korea ta arewa ba. Ko kuma ya shafi harkokin tattalin arzikin kasar ba.
A ranar jumaar data gabata ne dai ne Kwamitin tsaro ta majilisar dinkin duniya ta amince da wani sabon takunkumi kan Korea ta Arewa.