Kasashen Duniya Na Bikin Tunawa Da Ranar Yaki Da Cutar Amosanin Jini

Wata ma'aikaciyar kiwon lafiya take auna yarinya karama.

Ranar Lahdi 19 ga watan Yuni kasashen duniya ke bikin tunawa da ranar yaki da cutar amosanin jini wacce ke daya daga cikin cututtukan da suka fi wahalar da jama’a a kasashe masu tasowa sakamakon karancin asibitoci da tsadar magunguna.

Sai dai gwamnatoci da masu hannu da shuni na kasa da kasa na iya bakin kokarinsu wajen daukar dawainiyar masu fama da wannan cuta.

Ranar yaki da cutar amosanin jini wani lokaci ne na fadakarwa da kuma tayar da gwamnatoci da kungiyoyi daga barci game da nuyin da ya rataya a wuyansu a kokarin cimma nasarar wannan yaki na ceton rayuka musamman a kasashe masu tasowa inda matsalar ta fi kamari.

Dr. Foureratou Issoufou ita ce shugabar cibiyar kula da masu fama da cutar amosanin jini da ke birnin Yamai, ta fadi cewa cutar sikila cuta ce da ke shafar jini wadda ake gada daga iyaye. Ta kuma ce akwai masu fama da cutar da yawa a Nijer da suke gani a cibiyarsu, hakazalika wasu da yawa daga kasashen waje kamar Burkina Faso, Mali, Ghana da sauransu na zuwa neman magani a Nijer.

Wasu da ke fama da cutar amosanin jini sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta kama daga magungunan jinya zuwa kula, da dai sauransu. Sun kuma yi kira ga hukumomin Nijer da su kara taimaka musu da magani.

Dr. Iliassou Idi Mainassara shi ne ministan kiwon lafiyar al’umma, ya ce daidai gwalgwado gwamnatin Nijer na bada tallafi kuma masu hannu da shuni na iya shigowa harkar don a taru a taimaka.

Albarkacin wannan rana ta 19 ga watan Yuni, cibiyar kula da masu fama da wannan cuta ta shirya wani gangami a birnin Yamai domin tattara gudummowar jini daga wajen jama’a, yayin da a dayan bangaren taron ya kasance wani lokaci na gwajin jini ga mutanen da ke bukatar sanin ko suna dauke da kwayar cutar ko kuma akasin haka.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasashen Duniya Na Bikin Tunawa Da Ranar Yaki Da Cutar Amosanin Jini