NIAMEY, NIGER - An fi samu cutar ne a kasashe masu tasowa sakamakon karancin asibitoci da tsadar magunguna duk kuwa da cewa gwamnatoci da masu hannu da shuni na kasa da kasa na iya bakin kokarinsu wajen daukar dawainiyar masu fama da wannan cuta.
Ranar yaki da cutar amosanin jini wani lokaci ne na fadakarwa da kuma tayar da gwamnatoci da kungiyoyi daga barci game da nauyin da ke rataye a wuyansu a kokarin cimma nasarar wannan yaki na ceton rayuwa musamman a kasashe masu tasowa inda matsalar ta fi kamari.
A hirar ta da Muryar Amurka, Dr Foureratou Issoufou shugabar cibiyar kula da masu fama da cutar amosanin jini dake birnin Yamai ta ce matsalar cutar da na girma a kasar Nijar.
A albarkacin wannan rana ta 19 ga watan Yuni cibiyar kula da masu fama da wannan cuta ta shirya wani gangami a birnin Yamai domin neman gudumuwar jini daga wajen jama’a yayin da a wani bangare taron ya kasance wani lokaci na gwajin jini ga mutanen dake bukatar sanin ko suna dauke da kwayar cutar kokuma akasin haka.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5