BAUCHI, NIGERIA - A jerin kasashen da suka yi fice a fagen wasan kwallon kafa, kasar Brazil ce a sahun gaba, Belgium ta biyu, Argentina ta uku, Faransa ta hudu, Ingila ta biyar, Sifaniya ta shida, Italiya ta bakwai, Netherland ta takwas, Portugal ta tara, a yayin da kasar Denmark ta zo matsayi na goma, a cewar hukumar FIFA.
Hukumar ta kuma ce a kasashen Afrika, kasar Senegal ita ce ta shatakwas a fagen tamaula a duniya, sai Morocco ta ashirin da biyu, Tunisia ta talatin, Najeriya ta talatin da daya, Kamaru ta talatin da takwas, Masar ta arba'in, sai kuma Algeria ta arba'in da daya.
A gefe guda kuma, yayin da Amaju Pinnick ke shirin sauka daga mukamin shugabancin hukumar kwallon kafa ta Najeriya da ake kira NFF a takaice, bayan shekara 8, hukumar na ci gaba da shirye shiryen zaben wanda zai maye gurbinsa da za a yi ranar 30 ga watan Satumba.
Ahmed Sani Toro, tsohon babban sakataren hukumar kwallon kafa a Najeriya, yace kwamitin zaben da hukumar ta kafa ya fidda sunayen masu neman takarar kujerar su daya, ciki har da ‘yan arewacin Najeriya shida. Ya kara da cewa ya zuwa yanzu zai yi wuya a yi hasashen wanda ake gani zai lashe zaben.
Saurari rahoton takaitattun labaran wasanni daga Abdulwahab Muhammad:
Your browser doesn’t support HTML5