Kwararu daga kasashen Afurka mambobin kungiyar APO ta masu arzikin man fetur sun fara gudanar da taro a jiya Talata a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer da nufin tattauna wasu mahimman batutuwa da suka shafi kasuwancin man fetur.
Bitar ayyukan da kungiyar APO ta gudanar akan maganar kare muradun kasashen Afrika masu arzikin man fetur da batun kaddamar da sabbin dokokin wannan kungiya na daga cikin mahimman batutuwan da kwararru za su tattauna a kansu a yayin wannan taro dake matsayin na share fagen zaman Majalisar Ministocin man fetur da za a yi a nan Yamai a gobe 19 ga watan Nuwamba 2020.
A shekarar 1987 ne kasashen Aljeriya da Angola da Benin da Kamaru da Kongo da Gabon da Libya da kuma Nigeria, su ka kafa kungiyar kasashen Afurka masu arzikin man fetur, bayan shafe shekaru 7 na tuntubar juna. Kungiyar ta APO, wace bangare ne na OPEC, ta kara samun shigowar wasu kasashe sama da 10 a shekarar 2017 saboda lura da kyawawan sakamakon da ta samar wajen kare hakkin nahiyar ta Afurka a fannin man fetur.
Darektan ofishin Ministan man fetur na Nijar, Mahamadou Abara, da ke jawabi a madadin Ministan na man fetur, ya bayyana cewa wannan zama na da mahimmanci kasancewarsa wani lokaci na nazarin rahoton ayyukan sakatariyar wannan kungiya.
Bayan tattaunawa ta tsawon kwanaki 2 kwararun na kungiyar kasashen APO za su gabatar da shawarwarin karshen taro ga Majalisar Ministocin Man Fetur da ke Shirin zama a gobe Alhamis, 19 ga watan Nuwamba a birnin na Yamai.
Ga Sule Barma da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5