Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rijiyar Kolmani Na Kan Gaba A Aikin Gano Mai A Arewacin Najeriya


ABUJA: NNPC
ABUJA: NNPC

Bayan ziyarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai yankin gano fetur a arewa tsakanin Bauchi da Gombe, rijiyar binciken fetur ta KOLMANI ta biyu ta yi fice a kafafen labaru wajen gano man fetir a arewacin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan rijiyar Kolmani ta farko da aka fara aiki a kanta a 1999 inda aka samu iskar gas, yanzu kuma aka toni fiye da kafa dubu 10 da muradun kaiwa kafa dubu 14,270 don kammala aikin rijiyar ta biyu.

Sabon shugaban kamfanin fetur Mele Kyari ya ci alwashin bunkasa kamfanin da irin wannan aiki kazalika da tada matatu 4 kafin karewar wa'adin mulkin shugaba Buhari a 2023.

Lamarin aikin gano man ya Kara fitowa fili ne a watan jiya yayin mika ragama a hukumance da tsohon shugaban kamfanin fetur NNPC Maikanti Kachalla Baru ya yi ga sabon shugaban Mele Kolo Kyari.

Bayanai daga aikin nemo man na nuna samuwar man a yankin Neja har zuwa tafkin Chadi wanda aikin ya samu tsaiko a yankin kan iyaka saboda illar Boko Haram da kan sace ko barazana ga rayuwar jami'an binciken man.

Alamu dai na nuna samun man zai zaburad da samun kudin shiga a arewa, a maimakon dogaro kacokan kan noma da kiwo

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu Elhikaya

Neman Fetur a Arewa-3:40"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG