Sadaukar da kai akan batun zaman lafiya na daga cikin halayyar da a yau ke ja wa marigayi Kofi Anan kyakyawar shaida daga jama’a bisa la’akari da yadda ya dage haikan wajen jawon hankalin shuwagabanin duniya kan mahimmancin warware rikici ta hanyar sulhu a maimakon amfani da karfin soja. Alkassimu Abdurrahman wani mai sharhi akan al’amuran yau da kullum yace abubuwan da suka faru a yankunan Serbia, lokuta ne da majalisar dinkin duniya ta fuskanci barazana kuma duka lokutan da Kofi Anan ke jagoranci ne, shiyasa ake ganin yayi kokari.
Haka shi ma Alh. Salissou Amadou wani dan rajin kare demokradiya ya bayyana shugabannincin Kofi Anan a matsayin wanda ya gudana cikin hikima da kwarewa ya kara da cewa yana daka cikin
Kofi Anan ya ziyarci jamhuriyar Nijer a shekarar 2005 a wani lokacin da kasar ke fama da karancin abinci inda ya yi amfani da matsayinsa na sakataren Majalisar Dinkin Duniya domin jan hankulan kasashen duniya su kai daukin cimaka wa jama’ar wannan kasa.
Sauri cikakken rahoton Souley Moumouni Barma
Your browser doesn’t support HTML5