Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Shirya Shiga Tsakanin Gwamnatin Afganistan Da Taliban


Mike Pompeo, Sakataren Harkokin Wajen Amurka
Mike Pompeo, Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Jiya Lahadi Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya ce kasarsa ashirye take ta ba da goyon baya tare shiga tsakanin gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban domin kawo zaman lafiya

Amurka tace a shirye take, ta bada goyon baya kuma kai tsaye ta shiga cikin shawarwari tsakanin gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban. Jiya Lahadi sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yayi wannan furuci, ranar da shugaban Afghanistan Ashraf Ghani, ya bada sanarwar dala dalan shiri ko kuma yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Tunda farko a jiya Lahadi, shugaba Ghani ya bada sanarwa tsagaita bude wuta na watani uku na kashin kanta da kungiyar Taliban, sa’o’i bayan hukumomin suka tabbatar kungiyar ta yan tawaye ta kai sumame wata gunduma dake arewacin kasar ta kama sojojin gwamnati da dama

Shugaban yace yau Litinin idan Allah ya yarda sojoji zasu daina fafatawa, matsawar suma yan tawaye sun mutunta ka’idodin yarjejeniyar tsagaita bude wutar

Tsagaita bude wutar tazo lokaci daya da bikin babar Sallah.

Nan da nan ba’a ji martain kungiyar Taliban akan wannan sanarwar da gwamnati ta bayar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG