Kasashen Afirka 4 A Wasan Cin Kofin Duniya FIFA U-20

Egypt Ghana Brazil U20 Soccer

Nahiyar Afirka na da kasashe hudu da ake fafatawa da su a wasan cin kofin matasa ‘yan kasa da shekaru ashirin na duniya FIFA U-20, kasashen da suka hada da Nijeriya, Ghana, Mali da Sanigal duk sun sami narar shiga rukuni na biyu a gasar.

Kungiyar ‘yan wasan Najeriya ta Flying Eagles sun lallasa kasar Hungary biyu da babu a safiyar jiya Lahadi, hakan ya sa suka zamo na biyu a bayan kasar Brazil, za su buga wasa da kasar Germany ranar Alhamis in Allah ya kaimu.

Ita kuma kasar Ghana ita ke gaba a rukunun su na B, tana gaban Austria alokacin da Argentina ta tafi gida. ‘yan wasan Black Satellites zasu buga wasa da kasar Mali a wasan rukuni mai zuwa, za’ayi wasan ne a babbar birinin tarayyar Wellington 10 ga watan Yuni.

Kasar Senegal wadda ta sha kashi a hannun Najeriya a wasan karshe na cin kofin nahiyar Afirka, ta zo na uku ne a group din su na C bayan kasar Portugal da Colombiya, zasu buga wasa da kasar Ukraine 10 ga watan Yuni a birnin Auckland.