Bayan kashin da kungiyar ‘yan wasan flying eagles suka sha a fafatawar su da Brazil a kokarin shiga gasar wasan cin kofin FIFA na ‘yan kasa da shekara ashirin na duniya, ‘yan wasan na flying Eagles sun lallasa ‘yan wasan Koriya ta Arewa da ci 4 – 0.
Da farkon wasan, kungiyar Flying Eagles bata gane kan wasan ba sai da tafiya tayi tafiya amma da aka dawo hutun rabin lokaci kamar yadda masu iya Magana suke cewa idan rawa ta canza dole kida ya canza.
Saviour Godwin Undid dan wasan Flying Eagles kawai sai ya jefa kwallon fari a ragar ‘yan wasan koriya ta Arewa.
Wannan Nasara ta daga kulob din na Flying Eales da maki uku wanda ya mayar da kulob din a matsayin da suke kokarin kutsawa, wato komawa cikin rukuni na E.
‘Yan wasan na Flying Eagles sunyi wasa kwarai bayan dawoowa hutun rabin lokaci wanda a irin lokacin ne Brazil ta sami galaba akan su a wasan da suka buga a kwanakin da suka wuce.