Kasashe Hudu zasuTaimakawa Kamaru Yaki Da Ta’addanci

Sojojin Chadi na kare iyakar Najeriya da Kamaru.

Kasashen Faransa da Canada da Congo da kuma Aljeriya sunce zasu marawa shugaban kasar Kamaru Paul Biya baya a yaki da kungiyar Boko Haram dake kai hare haren ta’addanci musamman a yankin Arewa mai nisa

Jakadun kasashen ne suka bayyana haka lokacin da suka kaiwaministan kasashen ketare na kasar Kamaru Jean Mbela Mbela takardun a ofishinsa dake birnin Yawunde, domin mikawa shugaban kasar. Sun dai bayyana irin yunkurin da gwamnatocin kasashensu ke yi na marawa kasar Kamaru baya a yaki da ta’addanci.

A cikin jawabinta jakadiyar kasar Faransa a kamaru Christine Robynson tace kasarta zata yi kokari gaya wajen taimakawa kasar Kamaru da dakarun tsaro, da kayayyakin yaki irin na zamani, da kuma bayarda labaru na sirri, kan yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Ta bayyana cewa, akwai yarjejeniya tsakanin kasar Faransa da kuma Kamaru na taimakawa da kayan yaki, musamman a duk lokacin da kasar ta Kamaru ta shiga yaki da wata kasa, ko irin yadda yanzu haka kasar take fama da mayakan Boko Haram.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Garba Lawal ya aiko da kasar Kamaru

Your browser doesn’t support HTML5

Kasashu hudu sun bayyana niyar taimakawa Kamaru-2"53