Gwamnatin kasar Amurka ta sake mikawa kasa jamhuriyar Kamaru gudunmawar motoci domin yakar ‘yan kungiyar Boko Haram, wanda yanzu haka Sojojin Kamaru da Sojojin taron dangi suke cin galaba akansu.
Wanda ya mikawa Ministan tsaron kasar ta jamhuriyar Kamaru Joseph Beti Asumo, gudunmawar shine jakadar shine jakadar kasar Amurka Michael Hoza, bikin dai na mika kyaututtukan an gudanar ne a babban barikin Sojoji dake babban kasar Yaounde.
Jakada Hoza, ya mikawa Ministan tsaro na kasar motocoi kirar akori kura guda 13, da Land Cruiser guda 5, da kuma manyan motoci daban daban guda 12, da manya manyan janareto kuda 6.
Mr. Hoza, ya ce wannan taimako Gwamnatin kasar Amurka ce ta bayar kuma ya ci gaba da cewa Amurka zat yi aiki da Gwamnatin kasar Kamaru kafada da kafada domin basu labarai na sirri, sai nan Amurka zata ci gaba da marawa Sojojin Kamaru baya domin yakar ‘yan ta’addan Boko Haram a fadin kasar baki daya yace wannan shine siyasar kasar Amurka da kawarta kasar jamhuriyar Kamaru.
Shima Ministan tsaron jamhuriyar Kamaru Joseph Beti Asumo, ya ce wadannan kayan aiki dole ne ayi aiki dasu ta hanyar daya dace domin cimma buri shugaban kasar ta Kamaru Mr. Paul Biya, na raba kasar da ‘yan kungiyar Boko Haram.