Kasashe 32 ke Halartar Taron Kolin Makamashi a Nijar

Wakilan zasu tattauna sabbin dabarun kyautata kasuwancin ma'adinan karkashin kasa da na man fetur a lokacin wannan taron da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya
Kasashe kimanin 32 ne suke halartar taron kolin makamashi wanda Hukumar raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya na tsawon kwanaki hudu a yamai, babban birnin jamhuriyar Nijar.

Wannan taron koli zai nazarci sabbin dabarun kyautata kasuwancin ma'adinan karkashin kasa da na man fetur, sannan kuma zai duba dalilan da suka sanya kasashen Afirka ba su cin moriyar irin dimbin albarkatun kasar da suka mallaka.

Haka kuma, wannan taron kolin na makamashi yana zuwa a daidai lokacin da Jamhuriyar Nijar take sake nazarin dokokinta na sarrafa ma'adinan karkashin kasa da kuma irin huldarta da kamfanonin kasashen waje dake gudanar da harkar tonon ma'adinai a cikin kasar.

Ministan makamashi da man fetur na Jamhuriyar Nijar, Foumakoye Gado, yace wannan taron koli zai ba kasar damar kasa kunne ga kasashen da suka riga ta fara gudanar da irin wadannan ayyuka na makamashi, ta yadda Nijar zata iya inganta irin ribar da take samu daga ayyukan hakar ma'adinai da makamashi, mai makon jira sai 'yar riba kadan da kamfanoni ke ba ta.

Kungiyoyin fararen hula masu fafutukar samarwa da kowane dan kasa makamashi a Nijar sun bayyana farin cikinsu da wannan taron kolin, su na masu fadin cewa an jima ana ci da gumin 'yan Nijar a vfannin makamashi da ma'adinai, inda kasashen waje suke cin moriyar albarkatun Nijar ta hannun kamfanoninsu, su kuwa 'yan kasar ke shan wahala.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Koli Kan Makamashi A Nijar - 2:56