Kasar Turkiya Zata Jira Shirin Trump Akan Syria

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Kasar Turkiyya tace ba zata yi saurin cewa wani abu ba game da shirin Shugaba Donald Trump na samar da wani wurin da zai zama tudun na tsira a kasar Syria ba.

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Turkiyya Huseyin Muftuoglu ya fada jiya a Alhamis cewa yana da kyau a dakaci sakamakon binciken da Shugaba Trump wanda zai umurci ma’aikatar tsaro da kuma ma’aikatar harkokin waje zasu gudanar tukuna, wanda hakan zaisa a samar da wani wuri da zai zama mafaka ga farar hular kasar, wadanda suke gudu daga tashe-tashen hankula da suke aukuwa a kasar ahalin yanzu

Kasar Turkiyya wadda ke da bakin iyaka da Syria, ta jima da ganin an samar da irin wannan wuri wanda zai zamo a matsayin tudun natsira, amma kuma tsohon shugaban kasar Amurka Barrack Obama bai goyi bayan wannan tsari ba, musammam ta yin la’akari da irin kalubalen dake tattare da kare irin wannan wuri zai kasance, ciki ko har da yiyuwar anfani da sojan kasa na Amurka domin ganin an samar da wani kebabben wurin da za’a hana shawagin jiragen sama.

Sai dai kuma duk da haka sai da kasar ta Turkiyya ta samar da wani yanki a cikin kasar ta Syria wanda ta kaddamar dashi ta sama da kasa diomin ganin ta fatattaki kungiyar ISIS a bakin iyakar kasar.

A can kasar Rasha ko, mai Magana da yawun shugaban kasar Dmitry Peskov ya fada wa manema labarai cewa, kawo yanzu gwamnatin Trump bata tuntubi Rasha ba akan wannan batu, sai yace ammafa wajibi ne a auna irin hadduran daka iya biyo bayan samar da irin wannan kebabben wuri, ba wai a cika wuri da batun ‘yan gudun hijira ba.