Kafofin yada labarai na Rasha sun bada rahotanni ana daf da fara shawarwari tsakanin kasashen Rasha da Iran da kuma Turkiya wadanda suka shirya taron sulhun. Rasha da Iran suna goyon bayan Syria a karkashin shugaba Assad, yayinda Turkiyya da Amurka suka goyi bayan 'yan tawaye da suke neman hambare Assad.
Shwarwarin da za'a fara yau Litinin, zasu fi maida hankali ne kan karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta da take aiki ahalin yanzu.
Yarjejeniyoyin tsagaita wuta a baya wadanda suke da sa hannun Amurka da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD duk suna wargajewa cikin hanzari, saboda nan da nan sassan da suke fada zasu keta yarjejeniyar su kuma aibunta juna.
Wakilin MDD na musamman kan rikicin na Syria Steffan de Mistura, yana cikin masu shawarwarin da ake jin zai kai gobe Talata.
Amurka zata tura dan kallo zuwa taron, jakadanta dake Kazakhstan, maimaikaon tawagar da Rasha da Turkiyya suka nema. Amurkan tana cewa saboda bisa dalilai na shirye shiryen karbar mulki ba zata iya tura tawaga ba.