Wani Ministan kasar Turkiyya yace kasarsu ba zata yi wata-wata ba wajen maida martani nan take, muddin Amurka ta kuskura ta saka mata wani sabon takunkumi wai don ita Turkiyyar na tsare da wani Fadan kirista a hannunta.
WASHINGTON D.C —
Kamfanin dillacin labaran Anadolu ya ruwaito Ministan ciniki na Turkiyya, Ruhsar Pekcan yana cewa tuni suka riga suka fara aiwatarda wannan martanin kamar yadda Kungiyar Ciniki ta Duniya (W-T-O) ta shata.
A jiya ne aka ji Sakataren Baitulmalin Amurka, Steven Mnuchin ya na bayyana shirin Amurka na kakabawa Turkiya karin matakan kuntatawa idan ta ci gaba da tsare wannan fadan na Amurka mai suna Pastor Andrew Brunson, wanda yafi shekaru 20 yana zaune a can Turkiyyar, wanda kuma hukumomin kasar ke zargi da cewa shi magoyin bayan Fethullah Gullen ne, watau mutumen da Turkiyya ke zargi da cewa shine jigon kitsa makircin juyin mulkin da aka so yi a kasar a shekarar 2016.