Hukumomi a Somaliya sun ce ana gab da fadawa cikin tsananin rashin abinci a wannan yankin da ya balle, yayin da gwamnati ta kuma kawo karshen ayyukan cigaba saboda ta fuskanci mummunan fari, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dabbobi da dama a yankin na gabashi.
WASHINGTON D.C —
Da ya ke magana da Muryar Amurka, a Hargeisa, Mataimakin Shugaban Somaliya, Abdurrahman Abdullahi Seylici, ya ce da alamar farin zai dada muni, ta yadda kasadar fadawa cikin matsalar karancin abinci ke ta karuwa.
Seylici, ya ce yankin na Somaliya, bai da isasshiyar dukiyar da zai iya fuskantar wannan farin, wanda ya addabi tattalin arziki sosai.
Ya ce hukumomi sun yanke shawarar dakatar da ayyukan cigaba don su yi tattalin abin da ya rage, ta yadda za su iya kasancewa a shirye da zarar matsalar farin ta kara muni.