Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uganda: Omona Na Kungiyar 'Yan Tawayen LRA Ya Mika Wuya


Mazauna yankunan Zemio a Kudu maso gabashin Jmahuriyar Tsakiyar Afrika na fuskantar barazanar hare-hare (VOA/Z. Baddorf)
Mazauna yankunan Zemio a Kudu maso gabashin Jmahuriyar Tsakiyar Afrika na fuskantar barazanar hare-hare (VOA/Z. Baddorf)

Rundunar sojan kasar Uganda ta ce wani na hannun daman shugaban kungiyar Lord Resistance Army Joseph Kony ya mika kan sa kwana daya bayan da Amurka ta ce za ta janye sojojin ta da suke fauratar 'yan kungiyar da suka yi kaurin suna.

Yau Alhamis jami’an rundunar sojan Uganda suka ce babban jami’in sadarwa na Mr. Kony, Micheal Omona ya mika kansa a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Mr Omona ya yi tsawon shekaru 23 a cikin kungiyar LRA bayan da kungiyar ta sace shi a 1994.

Jiya Laraba rundunar sojan Amurka ta ce za ta janye rundunar sojan da aka kafa a shekara ta 2013 domin farautar mayakan kungiyar LRA da suke gararamba a Afrika ta tsakiya a kuma hukunta shugaban kungiyar Mr Kony da sauran jagororin kungiyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG