Rundunar hadin gwiwa da kasar Saudiyya ke jagoranta wadda ke yaki da masu tada kayar baya na kungiyar Houthi a Yemen ta ce zata kulle hanyoyin shiga Yemen ta kasa da ruwa da kuma filayen sauka da tashin jiragen na wani dan lokaci, yayin da take zargin kasar Iran da hannu wajan kai harin makami mai linzami a Riyadh.
Rahotannin hadin gwiwa da kafar sadarwar gwamnatin Saudiyya ta fitar yau litini, sun bayyana cewa za a rufe iyakokinne domin inganta sababbin matakan da aka dauka na sa ido domin gano yadda makamai masu linzami da sauran kayan soji ke kai hannun kungiyar Houthi, amma za a kula da yadda kungiyoyin da ke kai taimakon daukin gaggawa zai su iya shiga.
Kasar Saudiyya da jima tana zargin kasar Iran da taimakawa masu tada kayar baya yaki da halartacciyar gwamnati, kasar Iran ta musanta zargin.