Aikin bada rigakafin na Kolera ta baki da hukumar kiwon lafiya ta WHO ke jagoranta yana auna kusan kananan yara dubu dari da tamani yan tsakanin shekaru daya zuwa biyar. Yaran zasu samu Karin wani rigakafin da zai kare su daga wasu cututtuka.
Yaran sun samu maganin a karon farko da aka kaddamar da aikin bada rigakafin a ranar goma ga watan Oktoba da ta shige. A wannan lokacin an baiwa mutane sama da dubu dari bakwai rigakafin ta bakinsu wandanda suka haura shekara daya.
Kakakin hukumar WHO Tarik Jasarevic yace ma’aikatar lafiyar zasu kuma bada rigakafin cutar shan inna ga yara yan shekaru biyar a cikin wannan aikin don kare su daga cutar da zata nakasa su.
Facebook Forum