Sarki Salman bin Abdulaziz ya fada a taron da ake gudanarwa ta yanar gizo cewa, “Samar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya shi ne babban zabin mu. Za mu iya yin komai domin aiki tare wajen cimma manufar kyautata al’amura, ta yadda zaman lafiya, kwanciyar hankali da zama tare za su wanzu a tsakanin jama’ar yankin.
“Jama’ar yankin” sun hada har da ‘yan kasar Israila, wadanda ‘yan kasar Saudiyya ba sa mu’amala da su. A makon da ya gabata Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashe bayan rattaba hannu akan yarjejeniyar Abraham, wadda za ta daidaita dangantaka tsakanin Isra’ila da Daular Larabawa da Bahrain cewa, Riyadh za ta bi sahu a “lokacin da ya dace.”
To sai dai a kalaman na sa a wajen taron na MDD, Sarki Salman ya jaddada dadaddiyar matsayar Saudiyya na goyon bayan sulhu tsakanin kasashe biyu na Isra’ila da Falasdinu, tare da tabbatar da Birnin Kudus a zaman babban birnin Falsdinu mai ‘yancin kan ta.
Haka kuma ya bayyana goyon bayan shirin zaman lafiya na kasashen Larabawa na shekara ta 2002, wanda yayi tanadin tabbatar da kasar Falasdinu, a zamam sharadin daidaita dangantaka da Isra’ila.