Shugaban kasar Rasha ya zargi sojin MDD masu tsaron lafiya da goyon bayan wani bangare a rikicin kasar Ivory Coast.
Shugaba Dmitry Medvedev yace sojin MDD dake kasar Ivory Coast sun wuce gona da iri kuma sun goyi bayan wani bangre, al’amarin dayace wani salo ne mai cike da tsananin hatsari.
Sakatare Janar na MDD Ban ki-moon yace hare-haren da sojin MDD suka kai basu sabawa kudurin da MDD ta zartas kwanan nan kan kasar Ivory Coast ba, kuma yace sun kai hare-haren ne da nufin hana sojin Gbagbo su farma farar hula. Mukarraban Mr. Gbagbo sun kalubalanci wannan bayani, suka ce sojin MDD da na farasna sun so a kashe shugaba Laurent Gbagbo.