Shugaba Barack Obama na Amurka ya kira sabon shugaban kasar Ivory Coast ko Cote Divoire, Alassane Ouattara, domin taya shi murnar kama aikin da yayi.
Fadar White House ta ce Mr. Obama ya buga ma Ouattara waya jiya talata, kwana guda a bayan da mayaka suka kama tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, wanda ya ki sauka daga kan mulki. Fadar ta White House ta ce Mr. Obama da Mr. Ouattara sun tattauna muhimmancin sake maido da harkar cinikayya domin sake tayar da tattalin arzikin kasar Ivory Coast.
Har ila yau ta ce sun yi magana a kan bukatar tabbatar da cewa an hukumta mutanen da suka kai hare-hare a lokacin rikicin siyasa, ba tare da yin la’akari da bangaren da suka goyi baya a lokacin rikicin siyasar ba.
Har ila yau a jiya talata, Faransa ta ce nan ba da jimawa ba zata ba kasar Ivory Coast dala miliyan 580 domin ta taimakawa al’ummarta wajen sake maido da ayyukan kyautata jin dadin jama’a tare da farfado da tattalin arzikin kasar.
Ministar kudi Christine Lagarde ta ce za a yi amfani da kudin wajen biyan bukatun fararen hula na gaggawa,da ayyuka a birnin Abdijan da kuma wasu ayyukan bukatun na jama’a. Babban sakataren Majalisar DinkinDuniya, Ban Ki-moon, yayi kira ga kasar Ivory Coast a jiya talata da ta rungumi wannan kyakkayawar dama mai cike da tarihi da ta samu wajen sasanta al’ummarta a bayan damke Mr. Gbagbo.
Mr. Ban ya ce yayi magana da shugaba Ouattara litinin, ya kuma jaddada bukatar tabbatar da cewa ba a dauki fansa a kan magoya bayan Mr. Gbagbo ba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce zata ci gaba da kare fararen hula tare da taimakawa gwamnati wajen sake maido da bin doka.