Gwamnatin kasar Mexico ta ce za ta ba da mazaunin ‘yan gudun hijira ga wani ayarin bakin haure daga kasashen yankin Amurka ta tsakiya, wadanda sakonnin shugaban Amurka Donald Trump a shafinsa na tweeter su ka tada musu hankali kwanan nan, akan bukatar shugaban ta karfafa iyakokin kasarsa.
A wata sanarwa daga ma’aikatun harkokin cikin gida da na waje na Mexico suka fidda jiya litinin, sun lura cewa ayarin jama’ar wadanda yawancin daga kasashen Guatemala, da Honduras, da El Salvador suka fito, sun taba yin irin wannan tafiyar ta ayari tun daga shekarar 2010, abinda ke janyo hankali akan ‘yancin ‘yan gudun hijira, musamman wadanda ke guje wa matsanancin yanayin rayuwa a kasashensu don neman mafaka a wasu wuraren.
“Manufofi akan baki na kasar Mexico na da karfi sosai, da su ke neman tabbatar da doka, da oda wajen shigowar baki da kuma mutunta ‘yancin jama’a a cewar sanarwar. Babu yanayin da gwamnatin Mexico ta yarda da shigar baki ba bisa ka’ida ba a kasar.