Kasar Kamaru Ta Hana Yara Kanana Aikin Hakan Zinari

Yara da matasa dake hakan zinari a yankin Batare Oya a gabashin kasar Kamaru

Hadarin da ya auku a ma'akatar zinari da ya rutsa da mutane 74 wadanda akasarinsu yara kanana ne da suka bar makarantunsu suka shiga aikin ya sa gwamnatin kasar ta fitar da sabuwar dokar

Kasar Kamaru tana kira ga yaran da suke barin karatu suna aiki a masana’antar hakar zinari da su daina yin hakan. Kasar ta kaddamar da wannan gangami ne biyo bayan wani rahoto da yace hatsari da aka yi a masana’antar hakar zinari ya kashe mutane 74 a cikin wannan shekara kuma galibin su, yara ne da ya kamata a ce suna makaranta. Ga fasara rahoton wakilin Muryar Amurka Moki Edwin Kindzeka daga garin Betare –Oya dake gabashin Kamaru.


Gungun wasu matasa Kamaru su biyar da wata yar gudun hijirar jamhuriyar Afrika ta tsakiyar guda, sun je bakin rafi suna neman zinari. Daya a cikin matasan tana goye da jinjiri a bayanta, cikin dauda ta tabo a tana neman zinari.


Wadannan matasa yan shekaru 11 ne zuwa 15, suna daga cikin yaran da suka daina zuwa makaranta suka shiga aikin neman zinari.


Matasan sun ce kamfanonin China suna biyan su dalar Amurka daya na aiki da suke musu, akwai kuma karin la’ada idan sun samu zinarin.


Hukumomin gwamnati sun fadawa mazauna yankin su daina hakar ramukar neman zinari a wurin. Amma tsananin bukatar kudi yasa ana yin watsi da umarni hukumomin, ciki har da yan gudun hijira da suke barin sansanoninsu da iyayensu da ya kamata a ce ‘ya’yansu suna zuwa makaranta.


Yves Bertrand Alienou babban jami’i ne a karamar hukumar yankin Lom da Djerem. Yana zuwa kauye kauye yana kirar mutane su daina hakar zinari kuma su maida ‘ya’yansu da suke cikin wannan aiki, makaranta.



Sakon na farko shine tausayawa daga hukumomin daga hukumomin da muke wakilta, amma batu mai muhimmanci, shine muna kira a gare su, su daina shiga wannan aiki mai hadari a wurin. Kamar yanda suka sani kuma suka ga cewa aikin na tattare da hadari.



Wani rahoto da gwamnati da masu bincike masu zaman kansu suka buga a cikin wata Yuli, sun ce hakar zinari ta kashe mutane 50 a gabashin Kamaru a bara. Amma kuma wannan adadi ya haura a cikin watannin shidan farkon wannan shekara zuwa fiye da 70.


A cikin hadari mafi muni, yan Kamaru tara da wani dan gudun hijirar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika guda ne hadarin ya kashe, yayin da ramin zinarin ya rubta akansu a garin Ngoura a watan Disemban bara.


Michel Pilo, shine hakimin wani Kauyen Mali, yace kamfanonin China ba albarakatunsu kadai suke warwasonsu ba, har da ‘ya’yansu.

Yace Kamfanonin Chinan basu ginwa yaransu makarantu. Idan kuma yaransu dake hakar zinari suka lalata ruwan tabkin da suke amfani da shi, su yan Chinan basu kokarin samar musu da wani madadin hanyar samun ruwa kamar gina musu rijiyoyin birtsatse. Yace mutane da dama sun samu rashin lafiya dalilin shan ruwan da aka lalata wasu kuma sun mutu a wani gocewar kasa.


Vincent Atangana, wani jamai’in Kamaru a kamfnin hakar zinari nay an China mai suna EXXIL, ya dora laifi ne a kan iyayn yara da suka kyale ‘ya’yanu suna aiki a ma’aikatun. Sai dai ya hakake akan cewa hakar zinar da kamfanonin China suke yi, ya taimaka cewa ci gaba a yankin.

Yace ana gina gidaje masu yawa da kayan zamani. Atangana yace a shekarun baya, ana sayar da mai a cikin gwangwanin ne, amma kuwa yanzu akwai gidajen mai. Yace ana gudanar da wadannan ayyukan ci gaba ne yayin da ake kokarin kafa masana’antar hakar zinarin, kamfanonin zasu yi abin da ya fi haka idan masana’antar ta yi karfi.


Alienou yace gwamnati ta yiwa iyaye kashedi kana kuma ta umarci kamfanonin Chinan da su daina daukar ma’aikata da shekarunsu bai wuce na zuwa makataranta ba. Amma kuma ganin yanda kamfanonin Chinan ke tsananin bukatar zinarin da kuma ake matukar bukatar aiyukan yi a gabashin kasar Kamaru, ba’a mutunta wannan bukata yadda ya kamata ba.