Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Hari Ya Halaka Mutane 4 Tare da Jikata Wasu 20 a Kasar Mali


Wurin harin da aka akai a garin Gao
Wurin harin da aka akai a garin Gao

Harin kunar bakin wake da aka auna akan dakarun Faransa a garin Gao cikin kasar Mali ya halaka akalla mutane hudu tare da jikata wasu 20 da suka hada da sojojin Faransa takwas

Akalla fararen hula hudu ne suka rasa rayukansu a wani hari da ya kaikaici dakarun Faransa, yayin da suke sintiri a Mali a jiya Lahadi, inji ma’aikatar tsaron kasar.

Mutum 20 ne a cewar ma’aikatar tsaro aka tabbatar da cewa sun jikkata, ciki har da dakarun Faransa su takwas.

Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, wanda ya faru kwanaki kadan bayan da masu tsauttsauran kishin addini suka kai wani samame a hedkwatar dakarun hadakar kasashen Afirka biyar da ke Bamako, inda suka halaka mutum shida.

Wani kakakin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ya ce Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin, ya kuma jaddada aniyar majalisar wajen ci gaba da ba da goyon baya tare da hadin gwiwar kasashen duniya, ga dakarun Mali da al’umar kasar domin ganin an daidaita kasar.

Hare-hare a kasar ta Mali sun zafafa ne, yayin da take shirin gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 29 ga watan Yuli.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG