Kasar Kamaru tana fuskantar hare hare daga kungiyar nan ta ‘yan Boko Haram, masamman ma ta bangaren jahar arewa mai nisa kamar birnin Marwa, Kwalfata da garin Mora sun eke cikin tsaka mai wuya.
Wadannan garuruwa dai suna kan iyakar kasashen da suke amfani da tafkin Chadi, kuma sun yi iyaka da kasar tarayyar Najeriya.
Wannan ma shi yasa yanzu haka shugaban kasar jamhuriyar Kamaru Paul Biya, ya dauki tsauraran matakai na yakar ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
Ya ce ba zai yarda da wasu kungiya na ‘yan ta’adda ba wadanda zasu bata masa kasa, kuma yana kokari na ganin cewa kasar sa da kasashen makwabta zasu zamu tsintsiya madaurinki daya domin cimma burin a kakkabe ‘yan kungiyar na Boko Haram.
Yanzu dai dakarun kasashen dake makwabtaka da tafkin Chadi, suna gumurzu a faggen daga yanzu ana ganin za’a ci galabar abokan gaban.
Kasar Kamaru ta tura manyan jiragen saman yaki domin yiwa abokan gaban lugudan wuta, zaratan Sojojin dai sun ce yanzu ‘yan Boko Haram, zasu zamo tarihi saboda babu sani babu sabo na ganin cewa sun gama da ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
Your browser doesn’t support HTML5