Ministan kudin kasar Ghana Kenneth Ofiri Atta ne ya gabatar da kasafin kudin na dalar Amurka biliyan 13.9, biliyan 61 kenan na kudin Ghana.
Kamar yadda aka saba, duk lokacin da aka karanta kasafin kudi akan sami mabambantan ra’ayoyi tsakanin bangaren gwamnati mai mulki da ‘yan adawa.
Alhaji Mahmud Cezar dan majalissa daga jam’iyyar NPP mai mulki, ya ce kasafin kudin ya tabo batun samar da ayyuka a fannoni dayawa musamman ta fannin gine-gine, da sufuri, da noma.
Shi kuma Alhaji Madi na jam’iyyar adawa ta NDC, cewa yayi, ai a lokacin mulkin gwamnatin shugaba John Dramani Mahama, ya samar da ayyuka da dama ta fannin gine-gine amma jam’iyyar adawa ta NPP a wancan lokacin ta ce hakan rashin iya aiki ne, sai ga shi yanzu jam’iyyar mai mulki tana so ta bi wannan hanyar wajen samar da ayyuka.
Ga karin bayani cikin sauti daga wakilin sashen Hausa Ridwan Abbas.
Your browser doesn’t support HTML5