Kasar China Ta Yi Tayin Farfado Da Tafkin Chadi

Tafkin Chadi

Yayin da tafkin Chadi ke ci gaba da samun koma baya, kasar China tayi tayin tallafawa kasashen yankin don sake farfado da tafkin.

Tafkin Chadi mai girman murabba’in kilomita Miliyan Biyu da Dubu Dari Hudu a baya, a ‘yan shekarunnan tafkin na ci gaba da samun koma baya, inda yake tsukewa ta yadda a halin yanzu bai wuce kilomita Dubu Dari Uku ba.

Wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina ya tambayi Ministan albarkatun ruwan Najeriya, Injiniya Sulaiman Husaini Adamu ko wanne mataki kasashen tafkin Chadin ke dauka? Inda yace tafkin Chadi ya kafe fiye da kashi 90 cikin 100 daga yanda yake shekaru 40 zuwa 50 da suka gabata, hakan yasa akwai kuduri da kasashen tafkin da a nemi dabarun yadda za a janyo ruwa daga wasu wurare don tabbatar da cewa tafkin bai kafe ba.

Ministan ruwan Najeriya yace tuni kasar China tayi tayin tallafawa, yanzu haka dai ana shirin a rattaba hannu don su zo suyi aikin cikin shekara daya, amma yanzu dai zasu kara bincike kafin su tabbar da cewa ko aikin zai yiwu ko bazai yiwu ba.

Saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasar China Ta Yi Tayin Farfado Da Tafkin Chadi - 2'26"