Kasar Aljeriya Ta Dakatar Da Ayyukan Raya Kasa A Wasu Kasashen Afirka

Shugaban Kasan Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune

Aljeriya ta fitar da Nijar da takwarorinta na kasashen Mali da Burkina Faso daga jerin kasashen da ke cin gajiyar shirinta na raya kasashensu bisa zargin su da neman kusanci da Maroko da basa jituwa da juna.

Shirin raya kasashen na kasar Aljeriya wanda ke kunshe da biliyoyin kudade ya tanadi bayar da bashi ga kasashen Afirka, ko tallafa masu ta hanyar aiwatar da ayyukan raya kasa da zuba jari a cikinsu.

Sai dai a yanzu, gwamnatin Aljeriya ta dauki matakin cire kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da Guinea Conakry da Moritaniya daga jerin kasashen da za su ci moriyar shirin nata.

Matakin na kasar Aljeriya ya zo ne kwanaki biyo bayan shirin kasar Nijar na anfani da tashar ruwan kasar domin shigo da kayayyaki cikin kasar ko fitar dasu.

Shirin raya kasashen Afirka na gudana ne a karkashin wani shiri ta hanyar wata gidauniya dake kunshe da biliyoyin kudade wanda ya tanadi bayar da bashi ga kasashen da kuma tallafa musu wajen aiwatar da ayyukan raya kasa da kuma zuba jari a cikin kasashensu.

Aljeriya ta dauki matakin cire wadannan kasashen ne bisa zargin su da neman kulla yarjejeniyar cinakayya da ta diplomasiyya tsakanin su da kasar Maroko da basa ga maciji da juna akan goyan bayan da kasar Aljeriya ke baiwa masu neman yancin gashin kai na yankin Polisariyo.

Masana harkokin yau da kullun irin su Abdourahamane Dikko na ganin wannan matakin da kasar Aljeria ta dauka, zai yi tasiri akan kasar Nijar duba da yadda Nijar ke fama da takunkuman karya tattalin arziki da ECOWAS ta sanya mata.

Wannan matakin na kasar Aljeria ya zo ne a daidai lokacin da kasar Nijar ke neman kulla dangantakar kasuwanci da ita don tayi anfani da tashar ruwan kasar wajen shigo da kayayyakin kasar ko fitar dasu zuwa kasashen ketare.

Jihar Agadas dake arewacin Nijar, da ta raba iyaka da kasar Aljeriya, tana daga cikin jihohin Nijar da suka fi cin gajiyar shirin na kasar a bangarori da dama to saidai kungiyoyin fafutuka sun bayyana cewa akwai bukatar hukumomin kasar Nijar su bi hanyoyin da suka dace.

Saurari cikakken rahoton Hamid Mahmoud.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasar Aljeriya Ta Dakatar Da Ayyukan Raya Kasa A Wasu Kasashen Afirka