Kasafin Kudin 2025 Zai Rage Hauhawar Farashi Zuwa Kaso 15 - Tinubu

Kayan abinci a kasuwar Najeriya

‘Yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki sakamakon yawaitar hauhawar farashin kayan masarufi da rashin tabbas a kasuwar musayar kudade da ta sanya canjin dala kaiwa Naira 1, 700 a baya-bayan nan.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa kasafin kudin kasar na 2025 ya yi hasashen raguwar hauhawar farashin kaya daga kaso 34.6 da take a yanzu zuwa kaso 15 cikin 100 a shekara mai kamawa.

Ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin gabatar da kasafin kudin Najeriya na 2025 na Naira tiriliyan 47.9 gaban zaman hadin gwiwar zaurukan majalisun dokokin kasar 2 a yau Laraba.

Har ila yau, shugaban yace harkar canjin dala za ta inganta daga kimanin naira 1, 700 zuwa 1, 500.

“Kasafin ya yi hasashen cewar hauhawar farashi za ta sauka da kaso 34.6 da take a yanzu zuwa kaso 15 cikin 100 a shekara mai kamawa yayin da harkar musayar kudin dala za ta inganta daga kimanin Naira 1, 700 zuwa 1, 500 kuma ana zaton yawan danyen man da najeriya zata rika hakowa a kowace rana ya kai tsakanin ganga miliyan 2 zuwa miliyan 2 da rabi,” a cewar Tinubu.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayin da yake gabatar da kasafin kudin Najeriya na 2025 na Naira tiriliyan 47.9 gaban zaman hadin gwiwar zaurukan majalisun dokokin kasar 2

Ya kara da cewar an dora hasashen ne a kan mizanin lura da abubuwan dake faruwa irinsu rage yawan albarkatun man fetur din da Najeriya ke shigowa dasu daga ketare da kara yawan fitar da tatattun albarkatun man da samun kaka mai kyau sakamakon ingantar yanayin tsaro da rage yawan dogaro akan shigo da kayan abinci.

‘Yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki sakamakon yawaitar hauhawar farashin kayan masarufi da rashin tabbas a kasuwar musayar kudade data sanya canjin dala kaiwa Naira 1, 700 a baya-bayan nan.

Jumlar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta karu zuwa kaso 34. 60 cikin 100 a watan Oktoban 2024, a cewar hukumar kididdigar kasar (NBS) a yau Litinin.

Ku Duba Wannan Ma Fannoni Da Ke Kan Gaba A Kasafin Kudin 2025 Da Shugaba Tinubu Ya Gabatar
Ku Duba Wannan Ma Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya Ta Karu A Watan Nuwamba

Hauhawar farashin ta watan Nuwamban ta bayyana samun karin maki 0.72 cikin 100 idan aka kwatanta da na watan Oktoban 2024, a cewar rahoton alkaluman auna farashin kayayyakin masarufi (CPI) na NBS na baya-bayan nan da ke auna yanayin sauyawar farashin kayayyakin amfanin yau da kullum.