Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa Majalisar dokokin Najeriya kasafin kudin shekara 2025 na Naira tiriliyan 47.916
An dauki tsauraran matakan tsaro a harabar Majalisar Dokokin kasar gabanin gabatar da kudurin kasafin kudin shekara 2025 din na kudi Naira tiriliyan 47.916
Da farko an tsara gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 a ranar Talata 17 ga Disamba, daga bisani aka canza zuwa Laraba 18 ga Disamba, 2024.
Hukumar gudanarwar rukunin saye da sayarwa a harabar Majalisar ta sanar da cewa ba za a bude kasuwanci ba, a lokacin gabatar da kasafin kudin.
An kuma sanar wa masu ziyara da ma’aikatan da ba su da wani muhimmanci a majalisar da su zauna a gida har sai bayan gabatar da kasafin kudin.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya jagoranci zaman hadin gwiwar tare da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas.
Kasafin dai shi ne irinsa na biyu da shugaban ke yi tun kama aikinsa a shekarar 2023.
Dandalin Mu Tattauna