An Kawo Karshen Taron Manyan Hafsoshin Soja Na Afirka

Babban Hafsan Sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai tare da Mataimakin Babban Hafsan Sojin Amurka, Janar James C. McConville.

A Najeriya an kawo karshen taron manyan hafsoshin sojojin Afirka da rundunar sojan Amurka ta shirya da zummar kawo karshen matsalar tsaro a nahiyar.

Da yake jawabin rufe taron babban kwamandan rundunar sojan Amurka dake Afirka Janar Eugene LeBoeuf, ya jaddada batun hadin kai da aiki tare tsakanin sojoji. Inda ya ce akwai kyakkyawar makoma da wata dama ta musamman ga abokan kawancensu muddin aka samu hadin kai.

Janar Eugene, ya ci gaba da cewa hanyar kawai da za a iya murkushe abokan gaba itace ta hanyar yin aiki tare bisa wani kwakkwaran kawance, tun tunkarar duk wani kalubalen tsaro wanda shine makasudin taron.

Shi kuma babban hafsan tsaron Najeriya, janar Abayomi Olonisakin ya nuna gamsuwarsa ga abubuwan a aka tattauna a taron. Wanda kuma ya ce wannan taro ka iya zama sanadiyar karfafawa sojojin Afirka su magance matsalar nahiyar da kansu.

Ya ci gaba da cewa banbance-banbancen dake Afirka da kuma karuwar barazanar tsaro daga kungiyoyin ‘yan ta’adda, na bukatar gina kwakkwarar kawance don magance matsalar kamar yadda ya kamata.

A cewar wani masanin tsaro Air Kwamanda Baba Gamawa, wannan taro ya zo daidai lokacin da ya dace, domin anyi shi lokacin da kasashen Afirka ke cikin matsala.

Taro na gaba za a yi shine a kasar Botswana a shekara mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Domin karin bayani saurari rahotan Hasssan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kawo Karshen Taron Manyan Hafsoshin Soja Na Afirka - 1'59"