Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsawa Ta Kashe Wasu Daliban Najeriya Uku a Kamaru


Tsawa
Tsawa

Wasu ‘daliban jami’ar Taraba uku sun mutu bayan da tsawa ta fada musu a wani gandun daji a kasar kamaru.

Tawagar ‘daliban jami’ar Taraba har guda 50 sun kai ziyarar neman karin ilimi kan namun daji a jihar Arewa ta kasar Kamaru.

‘Dalibai uku sun gamu da ajalinsu bayan da tsawa ta fadowa bishiyar da suka labe yayin da ake kwarara ruwan sama.

Haka kuma ‘dalibai 16 sun sami raunika a dalilin faduwar bishiyar. Cikin wadanda suka mutu akwai namiji ‘daya mata biyu.

Gwamnan jihar Arewa ya tura da motar agaji inda aka kwashe ‘daliban zuwa Asibiti tare da basu kulawar ta musamman.

A cewar mai baiwa gwamnan shawara Mista Roul, sun yi iya bakin kokarinsu damin basu kulawar da ta kamata, yanzu haka sun mayar da ‘daliban Najeriya. haka kuma suna mika ta’aziyarsu ga iyayen yaran da ma gwamnatin Najeriya.

Domin karin bayani saurari rahotan Awwal Garba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG