A wata jaridarta ta mako-mako, kungiyar ISIS ta yi shelar nada Abu Musab al-Barnawi a matsayin gwamnan Daular ISIS shiyyar Yammacin Afirka (ISWAP), wadda aka fi sani da Boko Haram.
Labarin, wanda aka buga a mujallar ISIS da ke fitowa a yanar internet, kai tsaye bai ce al-Barnawi ya maye shugaba mai cika bakinan nan, wanda ya jagoranci kungiyar tun daga 2009, wato Abubakar Shekau ba, to amma biri ya yi kama da mutum tunda al-Barnawi ne ISIS ke dauka matsayin Shugaban Boko Haram.
Tuni al-Barnawi ya fitar da wani faifan bidiyo inda ya ke sukar Shekau, kamar yadda kafar labarai ta Sahara ya ruwaito. A rahoton, al-Barnawi ya caccaki Shekau, ya zarge shi da zama cikin ni'ima yayin da mata da yara ke fama da yunwa.
To saidai kuma wani wanda ya bayyana kansa da Shekau ya mai da martani kan abin da ya kira yinkurin juyin mulki a wani faifan bidiyo na minti 10 dauke da muryarsa, wanda aka sa a kafar YouTube na lokaci kankani kafin aka kawar. A faifan bidiyon, Shekau ya sake jaddada ikonsa kan kngiyar Boko Haram sannan ya ce al-Barnawi, wanda dadadden dan kungiyar ne, na kokari ne ya kawo rudami cikin kungiyar.