Wannan na faruwa ne dai dai lokacin da bangarorin Majalisar masu sabanin ra’ayi kan bayyana cewa wannan ne da gaskiya, ko wancan bashi da gaskiya. Sai dai kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, yace ba wani laifi da shugabannin Majalisar suka aikata kan batun, don haka ba zai amsa kiran wasu da suke neman ya yi murabus ba.
A lokacin da ‘yan jarida ke yiwa Dogara tambaya kan wannan takaddamar a fadar shugaban kasa, yace, “na karanta ka’idar shari’a kuma ni ‘dan Majalisa ne, ban san inda aka ce cusa wani abu a kasafin kudi laifi ba ne, ku ‘yan jarida sai kuje ku bincika.”
Dogara ya kara da cewa ba ya cikin wata damuwa, kuma ba shi bane shugaban kwamitin ladabtarwa na Majalisa ba balle ya fadi cewa za a hukunta ‘dan Majalisa mai wannan zargi Abdulmuminu Jibrin, ko ko a’a.
Daga batun kotun ‘da’ar ma’aikata kan shari’ar shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, zuwa wannan takaddamar ta Majalisar Wakilai, hakan na kawo cikas ga nasarar aikin Majalisar Dokokin Najeriya ta Takwas.
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.