Musamman ma a wannan lokaci da ruwa ya karewa dan kada a tsakanin ‘yan ta’addar da suka sami matsalar rarrabuwar kai. Rahotannin baya-bayan nan dai sun nuna yadda aka sami takaddama tsakanin shugabanin nan Boko Haram.
Inda wajen mutane 3 kowa ke jin shine ne shugaba, ko kuma tawagarsa ce tsantsar Boko Haram. Wanda har wasunsu sun kira junansu da an sami Kawarijawa, ma’ana ‘yan a ware.
Haka kuma Janar Rabe ya jaddada cewa sai inda karfinsu ya kare wajen tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a daga ta’addancin Boko Haram.
Masana harkar tsaro irin su tsohon sojan sama Ahmed Tijjani Rabo Gamawa yayi tsokacin cewa, ai yanzu mayakan boko haram shure-shure kawai suke yi wanda baya hana mutuwa.
Domin kuwa yace farfaganda kadai ta rage musu don nunawa mutane cewa har yanzu suna nan da karfinsu alhali kuwa sun fadi kasa warwas.
Shima mai fashin bakin al’amuran yau da kullum Hassan Gimba Ahmed, ya bayyana cewa wannan ishara ce ga mabiya Boko Haram.
Wakilinmu a Abuja Hassan Maina Kaina ne ya aiko mana da cikakken wannan rahoton da ke makalar kasa.